1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazana a taron Geneva na biyu

January 24, 2014

Wakilan gwamnatin kasar Siriya a taron Geneva da aka dade ana canzawa rana sunyi barazanar kauracewa taron.

https://p.dw.com/p/1Awib
Hoto: picture-alliance/AA

Taron na Geneva dai wanda aka fara shi a ranar 22 ga wanna wata na Janairu, ana sa ran za a dauki tsahon mako guda ana gudanar da shi. Sai dai wakilan gwamnatin ta Siriya sunce za su kauracewa taron in har ba mayar da hankali kan tattauna abubuwan da suke da muhimmanci ba. Ministan harkokin waje na kasar ta Siriya Walid al-Moallem ne ya bayyana hakan yayin ganawar da suka yi da jakadan Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasashen Larbawa kan yakin na Siriya Lakhdar Ibrahimi a kebance a taron na Geneva.

A nan gaba a yau ne dai ake sa ran Brahimi zai gana da wakilan 'yan tawayen a hannu guda. Ganarwar tasa da bangarorin da ke yakar juna sama da shekaru biyun da suka gabata a kebance dai, ya biyo bayan kin amincewa da suka yi su yi tattaunawar gaba da gaba a taron na Geneva da a baya aka shirya za su yi. Su dai 'yan tawayen sun dage kan cewa dolene Shugaba Bashar 'al-Assad na Siriyan ya sauka tare da kafa gwamnatin rikon kwarya, batun da bangaren gwamnatin suka sa kafa suka yi fatali da shi suna masu cewa ba abu ne mai yiwuwa ba.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman