Baraka tsakanin jam′iyyun kawance a Nijar | Siyasa | DW | 28.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Baraka tsakanin jam'iyyun kawance a Nijar

Daya daga cikin abokan tafiyar shugaba Issoufou a gwamnati mai ci, ya ce zai kalubalanceshi a zaben shugaban kasa da zai gudana a shekara ta 2016 mai zuwa.

Wannan sabuwar baraka na zuwa ne a yayin da ake tsamanin daukacin jam'iyyun da ke gungun kawancen masu mulki na shirin tsayar da dan takara daya, domin lashe zaben shugaban kasa.

To amma sai dai ba zato ba tsammani wani daga abokanan kawancen jam'iyyun ya bayyana anniyarsa ta tsayawa takara domin kalubalantar shugaban kasar. Sai dai jam'iyyar da ke mulki ta PNDS ta ce hakan ba zai bata tsoro ba.


Koda yake kawo yanzu ba'a kai ga raba gari ba tsakankanin gungun na jam'iyyun hadaka da ke jan ragamar mulkin kasar ta Nijar ba kalamai da wasu alamomin da abokanan tafiyar kawancen ke yi, na tabbatar da samun barakar da ke iya tasiri wajen bai wa ko wace jam'iyyar da ke da hali tsayar da takararta a zaben shugaban kasa mai zuwa, domin kalubalantar shugaban kasa Issoufou Muhamadu.

Shi ne dai mutumin da ake hasashen jam'iyyar PNDS za ta tsayar da shi dan takara saboda sake darewa a kan wa'adi na biyu na mulkin kasar. Daga cikin wadanda suke nuna alamomin barkewar barakar a tafiyar kawancen na MRN har da Alhaji Tahiru Gimba, shugaban jam'iyyar Model ma'aikata da ya jagoranci wani taron manema labarai wanda a cikinsa ya ce kawancen nasu na MRN na fuskantar wata mumunar matsala.


Tuni dai Alhaji Tahiru Gimban ya ce a shirye yake domin kalubalantar shugaban kasar ta Nijar a zaben 2016 masu zuwa domin magance wasu kura-kuran da ya fahimci kawancen da ke mulki na yi wa kasar musamman ma shugaban kasa ta hanyar zartar da wasu aiyukan da basu da amfani ga 'yan Nijar.

Sauti da bidiyo akan labarin