Baraka a huldar Najeriya da Afirka ta kudu | Labarai | DW | 26.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Baraka a huldar Najeriya da Afirka ta kudu

Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwarta kan kyamar baki da ke faruwa a kasar Afirka ta kudu, inda hakan ya kai ga kiran jakadanta gida don tattaunawa.

Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta bayyana cewa, ganin an yi makwanni uku da fara boren adawa ga 'yan cirani, inda aka hallaka mutane bakwai, hakan ya nuna makomar 'yan kasashen waje na cikin hatsari a Afirka ta kudu.

Sanawar ta kara da cewa jakadan Najeriya a Pretoria da kuma karamin jakadan da ke Johannesburg, an kirasu Abuja domin tattaunawa. Hukumomin Najeriya dai suka ce, bisa martani kan kyamar baki da yanzu haka ke gudana a kasar ta Afirka ta kudu ya zama wajibi a duba matakin da za a dauka.

Dama dai 'yan majalisar dokokin Tarayyar Najeriya, sun bukaci gwamnatin Afirka ta kudu ta biya diyya ga 'yan kasuwa da zauna gari banza da suka lalata musu dukiya.