Barack Obama ya ziyarci Thailand | Labarai | DW | 18.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Barack Obama ya ziyarci Thailand

A ƙasa da makonni biyu da sake zaɓen shugaban Amurkan ya soma ziyara a cikin ƙasashen yankin Asiya

Shugaba Obama dai ya gana da shugaba Yingluck Shinawatra wanda suka tattauna batutuwa da dama kafin daga bisani su yi wani taron manema labarai na haɗi gwiwa.wanda a ciki suka ambato batun tattalin arziki da hulɗa tsakanin ƙasashen biyu

Baya ga Thailand Obama zai ziyarci ƙasashen Bama da Kambojiya,inda a ranar Talata mai zuwa ake buɗe taron shugabanin ƙasashen yankin Asiya.Zai yi kuma amfani da wannan dama, domin ganawa da shugaban gwamnatin China Wen Jiabao.Ziyarar ƙasar Bama na matsayin abun tarihi a ma'amalarta da Amurka, kasancewar Barack Obama shine shugaban Amurka na farko da ke bisa gadon mulki, wanda ya taɓa kai ziyara a wannan ƙasa.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman