Bankwana da shugaban Sashen Hausa na DW | Zamantakewa | DW | 01.07.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bankwana da shugaban Sashen Hausa na DW

Yayin da Sashen Hausa na DW da ke birnin Bonn a Jamus ke bankwana da shugaban sashen, masu sauraro sun nuna kaduwa.

Moesch Thomas Kommentarbild App

Shugaban Sashen Hausa na DW mai barin gado, Malam Thomas Mösch

Masu sauraran tashar DW Hausa tare da masu bibiyar tashar ta kafafen sada zumunta na zamani kamar Facebook, sun nuna kaduwar tasu ne bayan suka kalli jawabin bankwana na shugaban Sashen Hausa na DW mai barin gado Malam Thomas Mösch kai tsaye a shafin Facebook na DW Hausan. Malam Mösch na bankwana da Sashen Hausa, bayan da ya kwashe shekaru 16 yana jagoranci. A karshen makon da ya gabata ne dai, ma'aikatan Sashen Hausan suka shirya tare da gudanar da wani bikin liyafar cin abincin dare domin yin bankwana ga shugaban mai barin gado.

Guppenbild Hausa Redaktion

Ma'aikatan Sashen Hausa na DW tare da shugabansu mai barin gado, Malam Thomas Mösch

Daruruwan masu sauraren DW Hausa da masu bibiyar tashar ta kafafen sadarwa na zamani irin su Kwamared Rilwanu Abdullahi shugaban kungiyar guragu a Najeriyar, sun tofa albarkacin bakinsu sakamakon irin kyakkyawar  alaka da mu'ammalarsu da shugaban mai barin gado. Ya kara da cewa suna yi masa fatan alheri, yana mai bayyana shi da mutum mai tausayi da ke sauraren koke-koken alu'mma ba tare da nuna wani bambanci ba. A yayin da yake jagoranci dai, shugaban mai barin gado ya kulla dangantaka da sauran kafafen yada labarai dabam-dabam a Najeriya da wasu kasahshen nahiyar Afrika, abin da ya sanya 'yan jarida da mawallafa majallu a Najeriyar kamar Alhaji Alhassan Abdullahi shugaban mujallar Abokiya ke nuna kaduwarsu ga komawar Thomas Mösch sashen bayar da horo ga 'yan jarida, inda ya ce yana yi masa fatan alkhairi.

Nigeria Übergabe FC-Bayern-Trikot an Quiz-Gewinner

Malam Thomas Mösch yayin da yake bayar da kyauta ga guda daga masu sauraronmu

Hajiya Hafsat Mohammed Mando ta kasance guda daga cikin masu sauraran tashar DW Hausa da ke kai ziyara ga shugaban a duk lokacin da yake a Najeriya, ta bayyana cewa ta girgiza matuka da samun labarin barin Malam Tanko wato Thomas Mösch Sashen Hausa na DW tana mai yi masa fatan alkahiri. Pastor Yohanna Buru da ke zama aboki ga shugaban Sashen Hausan mai barin gado da kuma ke sauraren dukkanin shirye-shiryen sashen, cewa ne ya yi Thomas Mösch abokin kowa ne. Yace yana da kyakkyawan salon mulki da ilmin zamantakewa da kuma taimakawa wajen karfafawa mata da matasa gwiwa su kama sana'o'in hannu dabam-dabam. Ya kara da jinjinawa DW da daukacin ma'aikatanta, bisa irin shirye-shiryen da suke gabatarwa da ke taimakawa wajen sauya rayuwar kungiyoyin matasa da ma al'umma bakai daya.

Sauti da bidiyo akan labarin