Banizuwela ta tura dakaru Yammacin kasar | Labarai | DW | 17.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Banizuwela ta tura dakaru Yammacin kasar

Vladimir Padrino Lopez ministan tsaro a kasar da ya ke jawabi a gidan talabijin na VTV ya bayyana cewa sun tura jami'an tsaro 2000, da sojoji na musamman 600 zuwa garin Tachira da ke iyaka da Kwalambiya.

Gwamnatin Banizuwela ta tura dakaru zuwa yankin da ke Yammacin kasar inda masu zanga-zanga ke afkawa gine-gine na jami'an tsaro da sace-sace a shaguna adaidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnati.

Vladimir Padrino Lopez ministan tsaro a kasar da ya ke jawabi a gidan talabijin na VTV ya bayyana cewa sun tura jami'an tsaro 2000, da sojoji na musamman 600 zuwa garin Tachira da ke iyaka da Kwalambiya.

Ya ce wannan umarni ne na Shugaba Nicolas Maduro bayan da ya lura da ci gaban tashin hankali a birnin San Cristobal hedikwatar jihar da ma wasu birane makota.

Zanga-zanga da rikici ya barke a fadin kasar sama da makonni shida saboda yadda al'umma ke ganin tasku sakamakon tabarbarewa ta tattalin atrziki da ake ci gaba da fiskanta a wannan kasa ta Banizuwela.