Bangui: Zaman dar-dar gabannin zabe | Siyasa | DW | 24.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bangui: Zaman dar-dar gabannin zabe

Al'ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na bayyana fargabarsu a game da yiwuwar barkewar tashin hankali a lokutan zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a karshen mako.

A ranar 27 ga wannan wata ne 'yan Jamhuriyar Afirka ta tsakiya kimanin miliyan biyu za su fito domin kada kuri'a zaben shugaban kasa da kuma na 'yan majalisa, sai dai kuma yanzu haka al'ummar kasar na cikin zaman dar-dar saboda yiwuwar barkewar rikici kamar yanda ta kasance a zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin milkin kasar a tsakiyar wannan wata na Disamba wanda ya yi nuni da irin raunin da ke tattare da matakan tsaro a kasar.

Symbolbild Verbrechen gegen die Menschlichkeit Zentralafrika

Mayakan sa kai na daga cikin wanda ake fargabar za su tada hankali lokutan zabuka.

Suma dai hukumomin rikon kwarya na kasar na nuna damuwarsu da halin da ake ciki wanda ke da nasaba da kin tabbatar da matakin karbe makamai daga hannun mayakan sa kai na kasar kamar yanda yarjejeniyar Bangui ta tanada. Anice Clement da ke zaman minista kana kakakin fadar shugaban kasa ya ce ''akwai tarin kalubale kafin a iya cimma nasarar gudanar da zaben cikin tsanaki domin yanzu haka har masu bukatar tafiya yakin neman zabe sun kasa shiga wasu yankunan kasar''.

Symbolbild französische Soldaten in Afrika

Sojojin kasashen waje sun ce za su tabbatar da tsaro lokacin zaben Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Kungiyoyin farar hula na kasar ma dai sun bi sahun gwamnati da sauran jama'a wajen nuna fargaba musamman ganin irin yanda ko baya ga birnin Bangui matsalar rashin tsaron ta yadu zuwa wasu yankunan kasar kamar su birnin Bambari na tsakiyar kasar abin da ke yin barazana ga shirin zaben. Yanzu dai al'ummar kasar dama na sauran kasashen Afirka sun zura ido su ga yanda wadannan zabuka za su gudana da irin tasirin da su yi.

Sauti da bidiyo akan labarin