Karfafa hulda tsakanin Rasha da hukumomin Bangui
August 21, 2018Talla
Hakan na zuwa ne 'yan kwanaki da kashe wasu 'yan jaridar kasar ta Rasha a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya wanda ya nunar a fili irin huldar da ke tsakanin kasashen biyu. Da yake magana bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar tare da takwararsa Marie-Noëlle Koyara ta Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, ministan tsaron kasar Rasha Sergueï Choïgou, ya ce burin shi ne na karfafa huldar tsaro tsakanin kasashen biyu.
Tun dai a farkon wannan shekara kasar Rasha ta aike da manyan sojojinta guda biyar tare da fararan hulla 170 masu bada horo, sannan kuma ta bayar da makammai ga gwamnatin kasar bayan da ta samu izini daga Majalisar Dinkin Duniya.