1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar inganta ilimin mata a Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 8, 2019

Mataimakiyar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Amina J. Mohammed ta yi kira ga karin tallafi a bangaren ilimin mata a Afirka, domin su cimma gajiyar tsarin kasuwanci mara shinge na kasashen Afirkan.

https://p.dw.com/p/3LllE
Amina Mohammed
Mataimakiyar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed Hoto: picture-alliance/empics/B. Lawless

A wata hira da ta yi da wakilinmu na Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar Mahaman Kanta a gefen taron kungiyar Tarayyar Afirka AU, Amina J. Mohammed da kuma ke zaman 'yar siyasa daga Tarayyar Najeriya, ta yaba da tsarin kasuwanci mara shingen da kasashen Afirkan suka kaddamar tare kuma da bukatar gaggauta tallafawa ilimin yara mata.