1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rayuka na salwanta a Bangaladash

Abdourahamane Hassane YB
January 2, 2019

A Bangaladash zaben 'yan majalisun dokokin da aka gudanar a ranar Lahadi da jam'iyyar Firaminista Sheikh Hasina ta samu nasara da gagarumin rinjaye, ya bar baya da kura bayan da bangaren adawa ya ce an tafka magudi.

https://p.dw.com/p/3Auim
Bangladesch Dhaka - Proteste nach Busunfall mit zwei Toten
Hoto: bdnews24/A. A. Momin

Dubban jama'ar Bangaladash ne suka gudanar da zanga zangar yin Allah wadai da abin da suka kira aringizo na kuri‘u da jam'iyar firaminista ta Bangladash Sheikh Hasina ta samu a zaben na ‘yan majalisun dokoki wanda ya gudana ranar Lahadi.

Jam'iyar ta la Awami League ta samu kujeru 288 daga cikin 300 da ake da su a majalisar dokokin yayin da jam‘iyyar ‘yan adawar ta BNP ta ce an yi kari da satar kuri'u da nuna barazana ga masu kada kuri'a da kule wasu magoya bayan 'yan adawa kusan dubu 15 a gidan kurku gabannin zaben tun daga ranar takwas ga watan Nuwamba.

Kamal Hossain shi ne jagoran hadin gwiwar wasu jam'iyun siyasar da wasu kungiyoyi masu fautuka watau Jatiya Oikyale ya ce sakamakon zaben ba zabin al’umma ba ne.

Bangladesch Dhaka Protest und Prozession mit symbolischem Sarg wg  Ermordung von Verlegern und Angriffen auf Blogger
Rayuka na salwanta a zanga-zangar adawaHoto: Imago/Z.H. Chowdhury

Sheikh Hasina 'yar shekaru 71 a duniya wannan shi ne karo na uku a jere da take samun wa'adin mulki tun daga shekara ta 2008, da ta samu rinjaye a zaben 'yan majalisun dokoki ta ce ko kadan ba ta da farga ba a game da sakamakon zabe tare da yin watsi da bukatar 'yan adawar na a sake gudanar da wani sabon zabe.

Kakakin jam'iyar ta Bangladesh Nationalist Party Syed Moazzem Hossain Alal ya ce sun gabatar da karar a gaban hukumar zabe a kan kujeru 221 wadanda ya ce dukkaninsu an tafka magudi sai dai kuma hukumar zaben ta y watsi da korafinsu.

Mutane sama da 20 suka mutu bayan tashin hankalin da a barke bayan zaben . Amirka da Majalisar Dinkin Duniya sun ce suna da ayyar tambaya a kan sahihancin zaben da wani kakakin MDD ya yi gargadin sasan biyu na Bangladash masu yin rikici kan sakamakon zaben da su nuna dattako.