1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karin magana da Salon magana

Yusuf BalaJanuary 24, 2016

Karin magana na zuwa ne da azanci me dauke da bangare biyu na maganar tamkar a bara gyada gida biyu.

https://p.dw.com/p/1Hj6x
Anschlag Nigeria Kano Bayero Universität
Kofar shiga jami'ar BayeroHoto: Reuters

Farfesa Abdulkadir Dan Gambo na sashin nazarin harsunan Najeriya a jami'ar Bayero da ke a Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya ya yi mana karin bayani:

Karin Magana da Salon Magana: Dukkaninsu abubuwa ne da ke cikin rukunin maganganu da muke kira Azanci ko hikima ta sarrafa harshe, to amma akwai banbanci tsakanin Karin magana da Salon magana, in an ce Karin magana irin tsarin nan ne na magana da ke zuwa da hikima kuma yakan dauki sifa da ke zuwa da bangare biyu wanda cikin maganganu na hikima shi ke daukar irin wannan salo. Akwai bangare na farko sannan akwai bangare na biyu, bangare na farko kanzo da wani bayani da ke zama a dunkule sannan bangare na biyu sai ya yi karin haske. Alal misali "Gaba ta kai ni" da "Gobarar Titi" wanda bangaren farko na Gaba ta kai ni ya zo da bayani ne a dunkule, sannan bangare na biyu Gobarar Titi ya yi karin haske. A karin magana bayanan kanzo gida biyu ne tamkar gyada ce a barata gida biyu. Sai dai a wasu lokutan bangare na biyun a kan shafe shi kamar misali "Lissafin dokin rano", wanda ya san wannan Karin magana ya san akwai bangare na biyunsa wato "Macacce da rayayye", duk kuwa da cewa ba a cika hadawa a fadi ba lokaci guda, amma haka ne cikon wannan Karin magana.

Salon magana kuwa kamar a ce azanci kawai, akwai hikima a maganar amma ba ta zuwa da salo irin na Karin magana,kamar a Zaurance "Yazadazo ma'ana yazo kenan, a na sassarka wasu gabobi na kalma ne dan isar da sakon da salo, wani misalin shi ne sadannidu wato sannu kenan ko wani misalin ana iya daukar kalmar farko a maida ta karshe misali likaco wato cokali da dai sauransu.

Nigeria Ramadan
Hausawa a lokacin hawan dabaHoto: picture-alliance/AP Photo/G. Osodi
Karte Nigeria Kano Dakasoye
Taswirar Najeriya na nuna jihar Kano da Abuja

Arishi da Habaici: Shi Arishi wata magana ce aka yi ta sai ta fado kan wani dace da aka yi ta a kansa, ba da niyya ba ne aka yi maganar sai dai ta fado a kan gaba. Shi kuwa Habaici an yi maganar ne dan a nuna cewa wani mutum ya yi wani abu mara kyau dan a muzantashi, misali a aji ne na makaranta wani ya saci agogo ko takalmi, me yin habaicin idan yazo zai iya cewa a jinmu yau mun samu wani dan bera, to da zarar wanda ya yi satar ya ji zai san da shi ake magana. Shi kuwa Habaici ana yinsa ne idan wanda ake so a batawa na wurin sabanin irin su Zambo da idan aka yi koda baya wajen wanda ya san mutumin zai iya fahimta tun da akan sako duk wasu alamu na mutumin yadda za a fahimci da shi ake maganar ba tare da kama suna ba.