Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da hari kan wata jami′a a Kenya | Labarai | DW | 02.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da hari kan wata jami'a a Kenya

Bayan ya mika ta'aziyarsa ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya ce za a taimaka wa Kenya ta shawo kan ayyukan ta'addanci.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da kakkausan lafazi da abin da ya kira harin da 'yan ta'addan kungiyar al-Shabaab ta kasar Somaliya suka kai kan jami'ar a Kenya inda suka halaka mutane da yawan gaske. Ban ya ce wadanda ke da hannu a wannan aika-aika za su fuskanci shari'a. Babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniyar ya yi fatan shawo kan lamarin cikin gaggawa ba tare da an yi wa wadanda ake garkuwa da su karin lahani ba. Ban ya mika ta'aziyarsa ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su sannan ya ce a shirye Majalisar Dinkin Duniya take ta taimaka wa Kenya wajen magance ayyukan ta'addanci da kuma tsattsauran ra'ayi.

Alkalumman da aka samu ya zuwa yammacin ranar Alhamis sun nuna cewa akalla dalibai 70 aka kashe sannan kusan 80 sun jikkata a harin da mayakan kungiyar al-Shabaab suka kai kan jami'ar da ke birnin Garissa na gabashin kasar ta Kenya.