Ban Ki-moon ya kai ziyara Gaza | Labarai | DW | 14.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ban Ki-moon ya kai ziyara Gaza

Sakatare Janar Majalisar Dinkin Duniya ya yi alkawarin sake gina Zirin gaza cikin gaggawa

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya kai ziyarar aiki na dan wani lokaci a wannan Talata zuwa yankin Zirin Gaza na Falasdinu, wanda yaki ya yi wa kaca-kaca, kwanaki biyu bayan kasashe masu ba da taimako sun yi alkawarin bayar da makudan kudade fiye da dala bilyan biyar, saboda sake gina yankin da ya wargaje lokaci fafatawa da dakarun Isra'ila.

Ban ya shiga yankin da mota har zuwa sansanin 'yan gudun hijira na Jabaliya, da ke zama daya daga cikin wuraren da Isra'ila ta yi matukar wargazawa. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi alkawarin ganin an yi amfani da kudaden cikin gaggawa ta hanyar da ta dace.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu