Bamanga Tukur ya ajiye muƙaminsa | Siyasa | DW | 15.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bamanga Tukur ya ajiye muƙaminsa

Yayin da rikicin jam'iyyar PDP ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa, hakan ya sa a yanzu shugaban jam'iyyar ta ƙasa ya yi murabus, inda yanzu aka shiga lalulbo wanda zai maye gurbinsa.

A ƙarshe dai shugaban jam'iyyar PDP da ke mulki a Tarrayar Najeriya Alhaji Bamanga Tukur, da ake ta yin taƙaddama a kan muƙaminsa bisa zarginsa da ke zaman dalilin dukkan rikicin da jam'iyyar ta samu kanta a ciki, ya ajiye muƙaminsa.

Wakilinmu Ubale Musa da ke Abuja fadar gwamnatin Najeriya, ya ce Alhaji Bamanga Tukur ya miƙa wa shugaban Najeriya Goodluck Jonathan takardar murabus ɗin.

Bayan raɗe-raɗin da aka daɗe ana yi kan hakan, inda kwanaki biyu da suka gabata, aka ba da rahoton cewar Bamangan na mai cewar shugaban ƙasar ba shi da hurumin korarsa daga muƙamin shugabancin jam'iyyar ta PDP.

Bayan murabus ɗin da Bamanga ya yi dai, a cikin daren yau Laraba, aka ƙira taron jiga-jigan jam'iyyar ta PDP a fadar shugaban ƙasa, inda aka tsara tarurruka daba-daban, domin gano bakin zaren rikicin jam'iyyar.

Dama can dai ko da gwamnoni bakwai da suka yi wa jam'iyyar ta PDP tawaye, suka ce sun yi haka ne bisa wasu dalilai da suka haɗa da rashin amincewar su da shugabancin jam'iyyar wanda Bamanga Tukur yake yi. Abin da kuma ya yi sanadiyyar ficewa gwamnoni biyar daga jam'iyyar, ciki har da gwamnan jihar Adamawa Admiral Murtala Nyako, wanda ya fito jiha ɗaya da Bamanga Tukur.

Daga ƙasa za a iya sauraron hirar da Lateefa Mustafa Jaffar ta yi da wakilinmu na Abuja Ubale Musa a kan batun

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Abdourrahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin