Bama: Kotun ta yi watsi da karar ′yan jarida | Labarai | DW | 23.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bama: Kotun ta yi watsi da karar 'yan jarida

Kotun kolin Myanmar ta yi watsi a wannan Talata da karar da 'yan jaridar nan guda biyu na kamfanin dillancin labaran Reuters suka daukaka a gabanta suna masu kalubalantar hukuncin zaman kaso na shekaru bakwai-bakwai.

Kotun kolin kasar Myanmar ta yi watsi a wannan Talata da karar da 'yan jaridar nan guda biyu na kamfanin dillancin labaran Reuters suka daukaka a gabanta suna masu kalubalantar hukuncin zaman kaso na shekaru bakwai-bakwai da wata kotun kasar ta yanke masu a baya a bisa samunsu da aikata laifuka masu nasaba da hada rahotanni kan rikicin 'yan Rohingyas. 

A wata sanarwa da ya wallafa, daya daga cikin lauyoyin da ke kare 'yan jaridar ya musanta zargin da ake yi wa 'yan jaridar yana mai kalubalantar kotun da ta fito da hujjojin da ke nuna 'yan jaridar sun aikata wani laifi. Zaman shari'ar dai ya wakana ba tare da an gabatar da 'yan jaridar Wa Lone dan shekaru 33 da kuma Kyaw Soe dan shekaru 29 a gaban kotun ba.

 Mahukuntan kasar ta Bama dai na zargin 'yan jaridar da mallakar wasu takardun sirri na wasu ayyuka da jami'an tsaro suka gudanar a jihar Rakhine ta Arewa maso yammacin kasar ta Bama inda jami'an tsaro suka halaka tarin Musulmi tsiraru 'yan kabilar Rohingyas.