Bama-bamai sun fashe a Iraki | Labarai | DW | 31.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bama-bamai sun fashe a Iraki

Akalla mutane 27 aka kashe kana wasu 53 suka jikata a cikin wasu jerin tagwayen hare-hare na kunar bakin wake a wata kasuwar da ke a birnin Bagadaza na Iraki a jajiberen bukukuwan shiga sabuwar shekara.

'Yan kunar bakin wake guda biyu ne suka tayar da bam a lokaci guda a kasuwar  ta sayar da karafan motocin daf da lokacin da masu saye da sayerwa suka yi cikar kwari a kasuwar.Hakmet Ahmed,na daya daga cikin jami'an da ke yin aikin agaji na gaggawa:

''Da muka ji karar fashewar abubuwan mun zo mun taras da gawarwakin mutane kwance cikin jini, jina-jina wasu wadanda suka samu raunika mun kawo musu dauki wasu kuma mun kaisu asibiti.''