Bama ba ta son a binciketa | Labarai | DW | 20.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bama ba ta son a binciketa

Hukumomin kasar Bama sun haramta wa kakakin musammun ta MDD isa kasar domin tantance gaskiyyar abin da ya faru.

 Yanghee Lee Kakakin Majalisar Dinkin Duniya

Yanghee Lee Kakakin Majalisar Dinkin Duniya

A cikin wata sanarwa da ta bayyana kakakin ta Majalisar Dinkin Duniya Yanghee Lee ta ce abin kunya ne haramcin da kasar ta Bama ta yi ma ta na shiga kasar, kuma hakan na nufin akwai wani abin da hukumomin na Bama ke boyewa. Fadan da aka yi tsakanin sojojin kasar ta Bama da 'yan kabilar Rohingya a yankin  Rakhine da ke a yammacin kasar a cikin watan Augusta da ya gabata. Ya yi sanadiyyar mutuwar rayukan jama'a da dama yayin da wasu suka fice daga matsugunansu.