1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afganistan: Bam ya kashe mutane a taron addini

Abdul-raheem Hassan
December 18, 2020

Ma'aikatar tsaron kasar ta ce maharan sun dasa bam a karkashin kujerar wata mota a tsakiyar birnin Ghazni da ke tsakanin birnin Kabul da Khandahar.

https://p.dw.com/p/3mvD3
Afghanistan Beerdigung Bettina Goislard 2003
Hoto: AFP/S. Marai

Hukumomin gwamnatin Afganistan sun tabbatar da mutuwar fararen hula akalla 15, wasu da dama sun jikkata a sabon harin bam da mayaka suka tayar yayin da al'ummar musulmi ke taron karatun Al-Kur'ani.

Babu kungiyar da ta dau alhakin harin kawo yanzu, sai dai dama dakarun gwamnati da mayakan Tliban sun sha dauki ba dadi a lardin Ghazni. Kuma sabon harin yazo ne bayan wani kazamin harin kunar bakin wake da ya kashe jami'an tsaro 30. Duk dai wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da gwamnati ke shirin sasantawa da mayakan Taliban.