Bam ya kashe mutane 50 a masallacin Mubi | Labarai | DW | 21.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bam ya kashe mutane 50 a masallacin Mubi

Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa sun tabbatar da mutuwar mutane 50, bayan da dan kunar bakin wake ya tarwatsa bam a cikin masallacin da ke karamar hukumar Mubi a jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Maharin mai kimanin shekaru 13 ya tashi bam da ke jikinsa a dai-dai lokacin sallar Asuba a cikin masallacin Madina da ke Unguwar Shuwa a cikin garin Mubi, rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta bakin kakainta Othman Abubakar a yayin zantarwarsa da DW ya ce ba sutabbatar da wadan da ke da hannu kan wannan hari ba, amma ya ce suna ci gaba da daukar matakan tsaro tare da killace wurin da abin ya faru don gudun abin da zai biyo baya.

Hukumar ba da agajin gaggawa reshen jihar Adamawa ta ce harin ya jikkata mutane da dama, kuma kawo yanzu ana ci gaba da ba su kulawar gaggawa a asibitoci da ke fadin garin. Karamar hukumar Mubi na a cikin kananan hukumomi da kungiyar Boko Haram ta kwace iko da su a shekarar 2014.