Bam ya hallaka mutane uku a Najeriya | Labarai | DW | 11.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bam ya hallaka mutane uku a Najeriya

Wani bam ya hallaka mutane uku tare da jikkata wasu guda tara a jihar Adamawa da ke Tarayyar Najeriya

Tashin bam a Adamawa ya sanya sabuwar fargaba

Tashin bam a Adamawa ya sanya sabuwar fargaba

Rahotanni da ke fitowa daga Yola fadar gwamnatin jihar ta Adamawa na nuni da cewa bam din ya tashi ne a daya daga cikin manyan sansanonin 'yan gudun hijira da ke yankin Malkohi. Wakilinmu na Yolan Muntaqa Ahiwa ya ruwaito cewa lamarin ya afku ne a dazu-dazun nan. Bayanai sun tabbatar da cewa bam din ya tashi ne a bayan wani dakin da 'yan gudun hijirar ke ciki sai dai ya shafi wadanda ke a wajen dakin ne kawai. Tuni dai mataimakin gwamnan jihar ta Adamawa Mr. Martins Babale da kwamishinan 'yan sanda da wasu kusoshin gwamnati suka ziyarci wajen tare da yin tur da lamarin. Harin dai na faruwa ne kwanaki kalilan da samun karin 'yan gudun hijira a wannan sansani.

Muntaqa Ahiwa/ LMJ Zainab Mohammed Abubakar