Bam ya hallaka mutane da dama a Yemen | Labarai | DW | 31.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bam ya hallaka mutane da dama a Yemen

Wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa bam, inda ya hallaka mutane a kalla 33, yayin da suke shagulgulan Maulidin wannan shekara birnin Ibb.

Dubban dalibai ne dai suka hallara domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhamadu S.A W. a wata cibiyar raya al'adu ta wannan kasa, yayin da wannan bam ya tarwatse a cewar wata majiya ta asibiti. A kalla dai gawarwakin mutane 20 ne da suka hada da mata da kananan yara, aka kwasa zuwa asibin Al-Thaura da ke birnin Ibb, yayin da aka kai wasu gawarwakin 13 a asibitin Al-Manar,. Harin kazalika ya kuma yi sanadiyar jikkatawasu mutane masu yawa ciki har da gwamnan jihar ta Ibb a cewar shaidun gani da ido.