Bam ya hallaka fiye da mutane 40 a Siriya | Labarai | DW | 27.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bam ya hallaka fiye da mutane 40 a Siriya

Wani hari da dan kunar-bakin-wake ya kai a wani gari na Kurdawa ya kai ga mutuwar fiye da mutane 40 a Siriya.

Fiye da mutane 40 sun hallaka wannan wasu da dama suka samu raunika sakamakon tayar da bam a wani garin Qamishli na galibin Kurdawa da ke kasar Siriya. Rahotannin kafofin yada labarai na kasar sun ce akwai yuwuwar samun karin wadanda suka hallaka, kuma kimanin 140 suka samu raunika.

Wani dan kunar bakin wake ya tayar da wannan bam kamar yadda hukumomi suka nunar. Fiye da mutane 240,000 suka hallaka sannan rabin al'umar kasar suka zama 'yan gudun hijira a ciki da wajen kasar ta Siriya, tun lokacin da rikici ya barke tsakanin dakarun Shugaba Bashar al-Assad da kuma masu neman kifar da gwamnatin da suke dauka ta kama karya.