Bam ya fashe a tashar manyan motoci ta Kano | Labarai | DW | 24.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bam ya fashe a tashar manyan motoci ta Kano

'Yan sandan a Jihar Kano da ke Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutum ɗaya kana wasu takwas suka jikkta, sakamakon fashewar bam a tashar manyan motoci a unguwar sabon gari.

shaidu sun ce wasu mutane guda biyu da suka saje da fasinja suka bar bam ɗin a cikin wata jaka. A shekarar da ta gabata ma dai an kai irin wannan harin bam a cikin wannan tasha wanda ya hallaka mutane da dama.

Kuma harin na zuwa ne kwana ɗaya bayan hare-haren ƙunar baƙin wake, wanda wasu 'yan bindiga suka kai a Kaduna wanda a ciki mutane da dama suka rasa rayukansu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar