Bam a taron jam′iyyar APC a jihar Rivers | Labarai | DW | 17.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bam a taron jam'iyyar APC a jihar Rivers

Wannan jiha dai na zama mahaifa ga matar shugaban kasar Goodluck Jonathan wato Patience Jonathan. Inda kuma siyasa ke da zafi tsakanin bangarori biyu na jam'iyyar PDP da APC.

An samu wasu abubuwan fashewa guda biyar da kararrakin bindiga a gangamin jam'iyyar adawa a garin Okrika a kudancin Najeriya a jihar Rivers mai arzikin man fetir a yau Talata inda mutane da dama suka sami raunika kamar yadda gwamnan jihar da shedun gani da ido suka bayyana.

Gwamnan jihar Rotimi Amaechi wanda kuma ke zama na bangaren jam'iyyar adawa ba ya wurin gangamin lokacin da abin ya faru.

Wannan gari kuma na zama mahaifa ga mai dakin shugaban kasar Goodluck Jonathan wato Patience Jonathan.

Jihar dai ta Rivers mai arzikin albarkatun man fetir na fiskantar tashe-tashen bama-bamai a daidai lokacin da ake ci gaba da tunkarar babban zaben kasar da ke tafe a ranar 28 ga watan Maris. Harin na yau dai an kai shi ne da nufin afkawa gangamin dan takarar gwamnan jihar ta Rivers karkashin jam'iyyar adawa ta APC wato Dakuku Peterside.