Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya gode wa Dattawan Arewacin Najeriya a bisa zabar sa cikin mutanen da suke son PDP ta tsayar da su takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP.
Kotun sauraren kara kan zaben shugaban kasa a Najeriya, ta ki amincewa da bukatar da jam'iyyun adawa suka gabatar mata na ta bari a yada zaman kotun kai tsaye.
An fara sauraron shari'ar kararrakin zaben shugaban kasa a Abuja inda jamiyyu biyar ke kalubalantar nasarar zababben shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu
Dan takarar shugaban kasa a Najeriya na babbar jamm'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar, wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasa ya kalubalanci nasarar da jam'iyya mai mulki ta yi.
A Najeria sannu a hankali ana samun karin sakamakon zaben shugaban kasar mafi yawan al'umma a Afirka duk da korafin jinkiri da damuwa da suka dabaibaye zukatan al'umma.