Bakin haure sun mamaye tsibirin Ceuta na Spain | Zamantakewa | DW | 27.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Bakin haure sun mamaye tsibirin Ceuta na Spain

Kasar Mokoro ta kasance daya daga cikin wuraren da bakin haure ke wucewa domin zuwa Turai

Mutuwar daruruwan bakin haure a cikin tekun Baharrun masu neman shiga Turai daga kasar Libiya, ya sake janyo hankalin kasashen duniya kan 'yan ci-rani daga kasashen Afirka masu neman zuwa kasashen Turai ko wasu wurare. Bakin haure kan shiga Turai ta Italiya da wasu kasashen Turan kamar Spain. A shekarar da ta gabata wani kiyasi ya nuna cewa kimanin 'yan kudu da Saharan Afirka 20,000 suka yi yunkurin shiga Turai daga Mokoro zuwa Spain.

Tsibirin Ceuta na kasar Spain ya zama daya daga cikin hanyoyin da bakin haure 'yan kasashen Afirka ke bi domin shiga nahiyar Turai daga kasar Mokoro. Tsibiran Ceuta da Melilla sun kasance basu da nisa daga Mokoro. Bakin haure da suka samu kai wa tsibirin kan nuna godiya saboda mutuwa da ake yi a cikin teku, kamar yadda Germinal Castillo na kungiyar ba da agaji ta Red Cross ya nunar.

Castillo ya kara da cewa an samu karuwar bakin haure saboda kasashen Turai sun rage kudaden taimako sakamakon matsalolin tattalin arziki. Bakin hauren da suka samu nasarar tsallakawa zuwa tsibirin na Ceuta suna samun kula na abinci, da tufafi gami da wurin kwanciya zuwa lokacin da mahukanta za su tantance makomarsu.

Abdubak Baba matashi yana cikin wadanda suka nuna gamsuwar shiga tsibirin na Ceuta da ke kasar Spain. Bakin haure daga kasashen Kudu da Sahara na Afirka kan shafe tsawon lokaci suna wuce kasashe kafin kai wa shiga jiragen ruwa na shiga Turai, inda wasu suke mutuwa a teku. Juan Antonio Delgado na kungiyoyi masu gadin gaban tekun Spain, ya bukaci kasashen Turai su kara zage damtse.

'Yan Afirka da ake gani a tsibirin Ceuta na kasar Spain suna cikin wadanda suka samu sa'ar shiga Turai da rai, yayin da wasu dubban suka mace a cikin tekun Baharrun. Mutuwar daruruwan bakin haure a gaban tekun Libiya ya kara fitowa fili da kasadar neman shiga Turai ko ta halin kaka.