Bakin haure sun kutsa yankin Ceuta na Spaniya | Labarai | DW | 07.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bakin haure sun kutsa yankin Ceuta na Spaniya

'Yan gudun hijira sun tsallake doguwar katangar wayoyi ta kan iyaka zuwa yankin Ceuta na kasar Spaniya.

Kimanin 'yan Afirka 190 ne suka kutsa yankin Ceuta na kasar Spaniya da ke gabar arewacin kasar Maroko. Shaidun ganin ido sun ce gungun bakin hauren sun shammaci dakarun tsaro na bangaren Maroko da Spaniya, lamarin da ya ba su damar kawar da shingen bincike na kan iyaka.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce tana kula da 'yan gudun hijirar da suka tsallake kan iyakar, ma'aikatanta kuma sun kai hudu daga cikinsu asibiti sakamakon raunin da suka samu a kokarin tsallake shingen kan iyakar mai katangar wayoyin kaya da ke da tsawon mita shida.

A kullum dai baki haure daga Afirka na kokarin shiga kasashen yankin tarayyar Turai ko dai ta teku ko kuma tsallake katangar a yankin na Ceuta.

Alkalumman da ma'aikatar cikin gidan Spaniya ta bayar sun ce a watannin shidan farko na wannan shekara bakin haure 3200 ne suka shiga yankunanta biyu wato Ceuta da Melilla, abin da ya ninka har sau biyu idan aka kwatanta da bara.