Bakin haure sama da 6000 sun kubuta a kusa da Libiya | Labarai | DW | 30.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bakin haure sama da 6000 sun kubuta a kusa da Libiya

A cewar kungiyar likitoci ta nagari na kowa MSF cikin wadanda aka ceto akwai yaro dan kwanaki biyar da haihuiwa baya ga wasu kananan yaran.

Mittelmeer Rettung von Flüchtlingen

Kasada ta ratsa teku dan kaiwa ga Turai lamari ne da ke zamewa duniya alakakai

Kimanin bakin haure 6500 ne aka samu damar ceton rayukansu bayan sun baro gabar teku a Libiya a ranar Litinin a cewar masu aikin sanya idanu kan masu fasakaurin al'umma ta ruwa a Italiya. Wannan rana dai ta kasance daya cikin wadanda aka fi samun aikin ceto a shekarun baya-bayan nan.

A cewar kungiyar likitoci ta nagari na kowa MSF cikin wadanda aka ceta akwai yaro dan kwanaki biyar da haihuwa baya ga wasu kananan yaran da aka daukesu da jirgin sama mai saukar ungulu zuwa wani asibiti a Italiya.Cibiyar da ta gudanar da wannan aikin ceto har sau 40 ta sami tallafi na jiragen aikin ceto daga Italiya da kungiyoyin agaji da jami'an aikin kula da gabar teku na Kungiyar Tarayyar Turai.