Bakin haure kimanin 700 sun mutu | Siyasa | DW | 19.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bakin haure kimanin 700 sun mutu

A ci-gaba da karuwar 'yan gudun hijira dake neman shigowa Turai, wani kwale-kwale da ya taso daga kasar Libiya ya nutse da cikin tekun Baharum ya hallaka mutane da yawa.

Kungiyar tarayyar Turai ta kira wani taron gaggawa bayan mutuwar daruruwan bakin haure cikin tekun na Bahrum. Shugaban kasar Faransa Francois Hollande, wanda ya yi kiran taron gaggawan, ya kwatanta abin da ya faru na mutuwar bakin haure kimanin 700 a rana guda, da cewar wannan shi ne bala'i mafi girma da aka samu bisa nitsewar da kwale-kwalen bakin haure da ake samu a tarihi, cikin shekarunnan.

Masu gadin gabar ruwan Italiya suka ce, mutanen da suka mutu bakin haure ne wadanda aka makare cikin wani karamin kwale-kwale wanda ya nutse da su gabannin isarsu tsibirin Lampedusa.

Mutane 28 ne dai kacal suka tsira, inda daya gada cikin wadanda suka tsira, ya ce jirgin ya kife ne lokacin da mutanen da ke cikinsa suka koma zuwa bangare guda na jirgin, a daidai lokacin da wani jirgi da suke zaton zai cece su ya nufo kusa da su. Kamar dai yadda Barbara Molinario, mai magan da yawun Humkumar kula da yan gudun hijra ta MDD a kasar Italiya ta tabbatar.

Italien Gipfel UkraineTreffen Angela Merkel und Matteo Renzi in Mailand

Angela Merkel ta Jamus da Matteo Renzi na Italiya"A lokacin da bakin hauren suka haggo jirgin ruwa mai dakon kaya yana isowa kusa da su, sai suka tsagu, kowa ya nemi fita kwale-kwalen don samun ceto. Kuma irin wadannan kwale-kwale da ke makare, idan mutane kadan suka girgiza, tana yiwuwa kwale-kwalen ya nutse. Daga nan kuma duk mutanen suka fada cikin ruwa, abinda ya faru kenan. Kuma kusan ba makawa wannan kwale-kwalen yana makare da mutane a lokacin da ya nitse."

Firaministan Italiya Matteo Renzi ya bayyana cewa akwai mamaki yadda kasashen duniya suka zuba ido, jama'a na mutuwa cikin teku, duk kuwa da ci-gaban zamani ta fannin na'urori da duniya ta samu.

"Ya zamu kasance bama damuwa bisa radadin mutuwar al'umma, wadanda ke rasa rayukansu, a lokacin da sadarwar duniya ta bamu damar shawo kan lamarin. Lokacin da na'urorin suke bamu damar sanin duk abin da ke faruwa. Ya zamu kasance kawunanmu a rabe bisa wannan lamarin"Babban abinda ya fi kawo cikas bisa daukar matakan bai daya tsakanin kasashen Turai a magance wannan matsalar dai, shi ne batun kudin tafiyar da aikin hana shigowa bakin hauren. Sai dai bisa wannan matakin dole shugabannin su dau sabbin matakai. Thomas de Maizière, ministan kula da harkokin cikin gidan kasar Jamus, ya yi tsokaci kan batun na mutuwar bakin haure.

"Tsarin da muka yi da farko an yi shi ne, bisa ceton gaggawa. Inda tsarin ya kasance wata gada tsakanin sama da mutane dubu dari da ke yunkurin tsallakowa Turai ta kan tekun Bahrum. Musamman daga kasar Libiya, da kuma 'yan-batagari da ke karban miliyoyin kudi suna makare jama'a cikin kwale-kwale suna hankadosu cikin teku. Wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane dubbai"

Wannan dai shi ne karo na biyu a 'yan kwanakin da suka gabata, da aka samu hatsari makamancin wannan. Hakan ne ma ya sanya ita ma kantomar harkokin wajen ta kungiyar EU Federica Mogherini ta ce ministocin harkokin waje na kungiyar ta EU za su tattauna don samo hanyoyin magance faruwar hakan a gobe Litinin. Bisa munin lamarin wannan karshen makon, taron na EU zai hada da ministocin harkokin waje da na cikin gidan kasashen EU. Inda ake saran daukar matakin magancen lamarin baki daya.


Sauti da bidiyo akan labarin