Bakin haure 30 sun hallaka kan hanyar zuwa Turai | Labarai | DW | 21.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bakin haure 30 sun hallaka kan hanyar zuwa Turai

Bakin haure 30 sun hallaka yayin da aka ceto 150 wadanda ke kan hanyar zuwa Turai kimanin mutane 600 aka makara a jirgin ruwan.

Wani jirgin ruwa dauke da bakin haure ya kife a gabashin gabar tekun kasar Masar, abin da ya janyo mutuwar mutane 30, yayin da aka ceto 150 da rai. Hukumomin Masar sun ce jirgin ruwan da ya tashi daga gabar ruwan kasar yana kan hanyar zuwa kasashen Turai ne.

Lamarin yana zuwa watanni bayan dakarun kare gabar kasashen Turai sun yi gargadin cewa bakin haure suna sauya barauniyar hanyar shiga Turai inda suka karkata ta Masar domin samun cika burinsu. Kimanin bakin haure 600 aka makara cikin jirgin ruwan lokacin da ya yi hadari.

Tun daga farkon wannan shekara fiye da mutane 1,800 suka gamu da ajalinsu a kokarin neman shiga kasashen Turai ta teku daga Afirka.