1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bakin haure 250 sun nutse cikin teku

March 24, 2017

Kimanin bakin haure 250 suka hallaka cikin tekun Bahar Rum sakamakon hadarin kananan jiragen ruwa biyu daga Libiya zuwa kasashen Turai.

https://p.dw.com/p/2Zrrr
Mittelmeer Schiffsunglück Flüchtlingsboot vor der libyschen Küste gesunken
Hoto: Getty Images/T.M. Puglia

Kimanin bakin haure 250 ake tsammani sun hallaka sakamakon hadarin da aka samu na wasu kananan jiragen ruwa guda biyu kan tekun tekun Bahar Rum.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa. Bakin hauren na kan hanyar daga Libiya zuwa Turai. Kawo yanzu gawawwaki biyar aka tsamo daga cikin tekun. Ana kayautata zaton kowanne daga cikin jiragen ruwan biyu na dauke da mutane kimanin 120 zuwa 140.

Wani kiyasi hukumar kula da 'yan gudun hijira Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa kimanin mutane 440 suka hallaka cikin tekun na Bahar Rum a kan hanyar zuwa kasashen Turai galibi 'yan Afirka lamarin ya ritsa da su.