Bakin haure 21 sun mutu a tekun Baharum | Labarai | DW | 06.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bakin haure 21 sun mutu a tekun Baharum

Bakin haure akalla 21 ne ake fargabar sun mutu a tekun Mediterranean, bayan da aka yi nasarar ceto wasu mutane saba'in da biyu daga cikin kwalekwalen da ya yi hadari a tsakiyar tekun.

Wata kungiyar bayar da agaji ta shaida cewa an kai wadanda suka tsira daga hadarin zuwa wani wuri da ke a tsibirin Sicily dake daf da gabar tekun.

A sanarwar da kungiyar ta fitar a jiya ta ce, daga cikin mutane da aka yanto, akwai wata mata mai juna biyu da kuma wasu yara kanana goma sha hudu da ke wannan bulaguro ba tare da rakiyar dangi ko iyaye ba. Akasarin bakin hauren da hadarin ya rutsa da su, sun fito ne daga kasashen yammancin Afrika.