Baki sun halaka a harin Afghanistan | Labarai | DW | 14.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Baki sun halaka a harin Afghanistan

Cikin wadanda harin ya halaka dai akwai 'yan kasar Indiya guda hudu da biyu 'yan Pakistan da dan Amirka da dan Italiya da Birtaniya

Mutane 14 mafi akasari 'yan kasashen waje sun halaka a wani hari da aka kai gidan saukar baki a birnin Kabul na kasar Afghanistan, harin da ya ritsa da mutane dama da ke halartar kallon wake-wake, abin da kuma ya jawo aka yi ta bata kashi tsakanin dakarun sojan kasar ta Afghanistan da masu tada kayar bayan, kamar yadda jami'ai a ranar Alhamis din nan suka bayyana.

Cikin wadanda harin ya halaka dai akwai 'yan kasar Indiya guda hudu da biyu 'yan Pakistan da dan Amirka da dan Italiya da Birtaniya da wani da ke da takardar zama a kasar Birtaniya da Afghanistan.

Harin dai ya ritsa da su ne da dare lokacin da suke halartar wani taron mawaka da ake saran wani sharararren mawaki daga kasar ta Afghanistan zai gabatar da wasa da sabbin wakoki.

Tuni dai kungiyar mayakan ta Taliban ta dauki alhakin kai wannan hari da ya dauki tsawon sa'oi bakwai ana fafatawa tsakaninsu da jami'n sojan gwamnati. Wannan fafatawa dai na zuwa ne adaidai lokacin da sojan kasar ta Afghanistan ke fuskantar babban kalubale na gudanar da aikinsu su kadai ba tare da tallafin sojojin kasa da kasa ba.