Bakar fata ta kafa tarihi a Jamus | Siyasa | DW | 05.07.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bakar fata ta kafa tarihi a Jamus

Aminata Toure Bajamushiya mai asali da Afirka ta kafa tarihi inda ta kasance 'yar Afirka ta farko da ta samu wakilici a gwamnatin jihar Schleswig-Holstein da ke arewacin Jamus.

Aminata Toure 'yar siyasar Jamus mai tushe da Afirka a Schleswig Holstein

Aminata Toure 'yar siyasar Jamus mai tushe da Afirka a Schleswig Holstein

Iyayen Aminata Toure sun yo gudun hijira daga kasarsu ta asali wato Mali zuwa Jamus, an haifeta ne a Jamus a shekarar 1992 kuma a sansanin da ake tsugunar da 'yan gudun hijira har sai da ta kai shekaru biyar tana rayuwa, kafin daga bisani ta samu shedar zama 'yar kasa tana da shekaru 12. Aminata ba bakuwa ba ce a fagen siyasar Jamus, don kuwa an taba zabarta mataimakiyar shugaban majalisar jaharta ta Schleswig-Holstein, nan ta soma kafa tarihi a matsayin bakar fata ta farko da aka zaba a mukamin kamar yadda kafafen yada labarai ke kwatantawa.

Toure ta shaidawa tashar DW cewa, tana daukar kanta a matsayin mai ruwa biyu wato bakar Bajamushiya inda ta ce "na ganin al'ummarmu a Jamus suna da bambance-bambance ba a siyasa kadai ba, domin a fagen siyasa yawancinsu maza ne, kuma Turawa ke da rinjaye, masu rinjaye kuma wadanda suka yi karatu da makamantansu ne, a matsayinmu na al’umma guda, tunaninmu yana da tasiri kan yadda muke yada manufarmu a siyasance. A ko da yaushe ina jina a tsakanin wacce ta fito daga nahiyoyi biyu, ba na son na yi zabi a tsakanin Jamus da Mali saboda haka na fi son a sanni da bakar Bajamushiya, don haka ina amfani da kalmar nan ta kungiyar mata bakaken fata da ke fafutuka a nan Jamus da aka fi sani da "Afro-German.''

Karin Bayani: Wacece Aminata Toure 'yar siyasar Jamus?

Jajircewar Toure a fagen siyasa da ta soma da fafutukar jan hankalin Jamusawa, ya soma ne daga irin kalubalen da iyayenta suka fuskanta daga gwamnatin Jamus na yunkurin mayar da su Mali, batun da ya samu gurbi a tunanin Aminata inda har ta yi kokarin ganin ta karanci kimiyyar siyasa a jami'a.

Aminata Toure 'yar siyasar Jamus mai tushe da Afirka a Schleswig Holstein

Aminata Toure 'yar siyasar Jamus mai tushe da Afirka a Schleswig Holstein

Ta shiga gwagwarmayar ganin ana bai wa bakakake 'yan gudun hijira 'yancin zama da kulawa a Jamus ba tare da an nuna musu wariya ba, amma baya ga haka iyayenta sun ci gaba da tunatar da ita cewa, idanun duniya na kanta saboda haka ta kara zage damtse fiye da takwarorinta Jamusawa a sauke nauyin da ya rataya a wuyanta musanman da wannan karin girman, abin da Aminata ke son ganin ta kawar kenan, a sami daidaito a tsakanin kowanne jinsi ba tare da an yi la'akari da launin fata ba.

"Ba a bu ba ne mai sauki, a ga mace na gwagwarmaya balle a ce mace bakar fata a cikin al’ummar da dukkansu fararen fata ne, akwai kalubale don na dandana dacin nuna min kyama don kawai na fito daga wata nahiya, amma a daya bangaren kuma na sami goyon baya."

Karin Bayani: Mace bakar fata ta farko a majalisar Jamus

 Aminata Toure ta san radadin nuna wa mutum kyama saboda kawai launin fatarsa, shi ya sa ta ci gaba da fafutukar ganin an kula da wadanda ake wa kallon 'yan tsiraru a kasar. A wani littafi da ta rubuta mai suna "We can be more'' a ciki ta nemi Jamusawa da su mutunta duk wadanda suka taimaka a gina kasar.

''Na baya da ke tasowa masu sha’awar siyasa ba za su fuskanci matsaloli a fagen siyasar Jamus ba, ba don a riga an bude musu hanya. Ya kamata Jamusawa su yi alfahari da gudumowar da duk wadanda suka bai mafaka a kasar suka bayar, wajen ginuwar demokradiyyarta da kuma wadanda har yanzu ba su nuna gajiyawa ba a karfafa kasar da mutunta dokokinta.

Ba na son ya kasance abin mamaki ga mace bakar fata a siyasar Jamus, ina son a saba ya kasance ba wani sabon abu ba ne."

Tarihi zai ci gaba da tuna Aminata Toure da fafutukarta ta kare 'yancin mata, musamman matasa 'yan ci-rani da yaki da nuna wariyar launin fata da kyawawan muradunta kan tsarin ilimi da kuma batutuwa da suka shafi shige da ficen Jamus.