1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baje kolin litattafai na farko a Kenya

Usman Shehu Usman AAI
October 22, 2019

Bikin baje kolin litattafai irinsa na farko a birnin Nairobi na kasar Kenya ya motsa sha'awar mawaka da marubuta daga nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/3Rjze
Symbolbild Bücher lesen
Hoto: Fotolia/Africa Studio

Bikin baje kolin da ya gudana a birnin Nairobi da ke kasar Kenya wanda kuma yazo a dai-dai lokacin da ake gunadar da makamancin irin taron a birnin Frankfurt da ke nan Jamus, ya sake tabo muhimmin batu na al'adar karatun litattafai ga 'yan Afirka, bincike dai ya gano cewar 'yan Afirka ba sa karatu sosai, wannan ne ma ya sa litattafai ke da tsada a nahiyar.

Hirar wani marubuci da wakilin DW a Kenya
Hirar wani marubuci da wakilin DW a KenyaHoto: DW/H. Mwilima

To amma yanzu sannu hankali lamarin ya sauya, inda ake samu kasashen Afirka da yawa mutane na matukar neman litattafan karatu. Daya daga cikin wadannan kasashen da ake daukin karatu ita ce Kenya, musamman a Nairobi babban birnin kasar inda cikin shekarun nan bukatar litattafan karatu ya yi matukar karuwa. Taron dai ya hada fitattun mawaka da marubuta a nahiyar ta Afirka kamar yadda za a iya saurara a sautin rahotonmu.