Baje kolin kayyakin kade-kaden gargajiya | Zamantakewa | DW | 24.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Baje kolin kayyakin kade-kaden gargajiya

Ma'aikatar lura da kiyaye al'adu ta Masar ta gudanar da bikin baje kolin kayyayyakin kade-kade da raye-rayen gargajiya don nuna muhimmancinsu wajen raya al'adu.

A daidai lokacin da matasa ke kara raja'a kan kade-kaden zamani sakamakon saukin sarrafasu da kuma bunkasar fasahar keresu, ma'aikatar lura da kiyaye al'adu ta Masar ta gudanar da bikin baje kolin kayyayyakin kade-kade da raye-rayen gargajiya na kasa da kasa don nuna mahimmancinsu wajen raya al'adu da kara dankon zumunci tsakanin al'umomin kasashen duniya.

Makada na nahiyoyin Afirka da Asiya da Turai da ma Amirka ta Arewa da Kudu sun cika makil a dandalin Qal'a da ke fadar Sarki Salahudeen wacce ke tsakiyar birnin Alkahira.

Farid el Atrache

Duk da banbancin harshe da ke tsakaninsu, su kan fahimci juna ta hanyar amon ganguna da sautin algaita da sarewa wadanda ke isar da sakon fatan samun zaman lafiya a illahirin doran duniya kamar yadda taken bikin baje kolin ke nuni.

Intisar Abdulfatah, shugaban shirya taron baje kolin ya bayyana irin mahimmancin da al'adun gargajiya ke da su wajan kara dankon zumanta da dinke barakar da ke tsakanin al'umomi da kabilu inda ya ke cewa ''a da ana kada ganga ne don ayyana yaki kan makiya amma yanzu mun mayar da amon ganga ya zamo ya na dauke da sakon soyayya da zaman lafiya. A wannan mawuyacin yanayi da duniya ke ciki akwai bukatar mawaka su kara goge makogwaronsu, makada ma su kwale gangunansu don ta da tsimin soyayya da da zumunta tsakanin mutane."

Ministan raya al'adun gargajiya na Masar Arab Auda wanda ya bude taron da jinjinawa babban bako a taron wato kasar Afirka wacca ya yi mata kirari da "jakadiyar rangwame da zaman lafiyar duniya" ya ce ita ma kasar Masar ba za a bar ta a baya ba wajen isar da sakon zaman lafiya a duniya ta hanyar tikar rawa da amon ganguna.

Shugaban tawagar mawakan Aljeriya, kasar da ta fuskanci yakin basasa na tsawon kusan shekaru goma ya bayyana irin rawar da kade-kaden gargajiya suka taka wajan dinke barakar dake tsakanin yan kasar.

Arabische Tanz und Musik

Ya ce "munzo don isar da sakon zaman lafiya ne kamar yadda mu kai nasarar tabbatar da shi a kasarmu. Ya kamata mu maye gurbin zage-zage da rera wakokin barkwanci, mu maye gurbin amon alburusai da amon ganguna da rawa da juyi. Kamar yadda muka dandana kudarmu sakamon yaki bama fatan ganin wasu al'umomin sun dandana ta su."

A gefe daya cikin fadar da ake baje kolin, kasashe sun kakkafa tantunan da cikinsu suka baje kayyakin kade kade da raye-raye na gargajiya.

A cikin tantin kabilar Nubawa da ke jihar Aswan ta Masar, an baje kayyakin kade-kade da suka samo tushe tun kusan shekaru dubu hudun da suka gabata, wato tun zamanin fir'aunoni.

Grace Wyoma, wata makidiyar bori da ta hallaci taron ta bayyana yadda karar garaya da rurin ganguna ke korar al'janu daga jikin marar lafiya kuma ya tsaftace kurwarsa daga cutattukan da suka gagari likitoci.

Ta ce "kida babban ginshike ne a tikar rawar da 'yan Afirka ke amfani da ita wajan magance jinyoyi. Akwai wasu karirrrika da amon ganguna na musamman da ke magance cutattuka na jiki da na kurwar daidaiku dama taron jama'a."

Instrumentenbauer im Irak - Traditionelle Laute (Oud)

Dabi Debo Ayanlola wani mawakin Najeria daga kabilar yarbawa na daga cikin wadanda suka halarci taro, ya kuma ce da fari ya na da mahimmanci ga 'yan uwana matasa su kwan da sanin cewa ba wanda zai kare musu al'adinsu muddin sukai watsi da ita suka rungumi wata.

Suma masu bandiri da ke wakokin addini da begen ma'aiki S.A.W ba a barsu a baya ba wajen nuna irin baiwar da mai duka ya yi musu.

A yayin da wasu 'yan kasar ta Masar ke daukar wannan biki a matsayin wata dama ta sanyaya zuciyar da damuwa ta dabaibayeta, wasunsu kuwa daukar sa suke a matsayin sharholiya da shagala a daidai lokacin da daruruwan 'yan kasar ke juyayin kashe danginsu da aka yi a rikicin siyasar kasar na baya-bayan nan.

Mawallafi: Mahmud Yaya Azare

Edita: Mohammad Nasiru Awal/Ahmed Salisu