Badakalar Shugaba Zuma ta ja hankalin jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 02.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Badakalar Shugaba Zuma ta ja hankalin jaridun Jamus

A sharhinta mai taken mafarkin Biafra, jaridar Die Tageszeitung ta yi tsokaci ne game da sako jagoran kungiyar Biafra Nnamdi Kanu daga gidan yari makonni hudu da suka wuce.

Bari mu fara sharhin jaridun na Jamus akan nahiyarmu ta Afirka da Jaridun Süddeutsche Zeitung da kuma Die Tageszeitung wadanda suka yi tsokaci akan dambarwar da ta dabaibaye shugaban Afirka ta kudu Jacon Zuma na sakonnin e-mail da suka bankado badakalar cin hanci da ake zargin shugaban da shirinsa na komawa Dubai idan ya bar mulki da kuma tsallake rijiya da baya da ya yi a kuri'ar rashin amanna daga 'yan majalisar dokoki na Jam'iyyarsa ta ANC.

Jaridar ta ce Zuma ya sake tsallake siratsi na sabon yunkurin tsige shi daga karagar mulki. Yunkurin da ya fito daga jam'iyyarsa ta ANC sakamakon wasu bayanan e-mail da suka nuna Zuma cikin badakalar cin hanci dumu dumu tsakaninsa da iyalan Gupta 'yan kasuwa 'yan kasar Indiya masu karfin tasiri da aka tsegunta wadanda kuma wasu jaridu biyu na Afirka ta Kudu suka wallafa.

Sakonnin email din sun nuna yadda yan kasuwar iyalan na Gupta suke juya akalar shugaban kasar da wasu ministocinsa. Tasirinsu ya dangana har ga hukumomin gwamnati. Bugu da kari e-mail din ya kuma nunar da yadda Shugaba Zuma yake shirin komawa Dubai a karshen wa'adin mulkinsa wanda aka ce iyalan na Gupta suka tsara masa.

A sharhinta mai taken mafarkin Biafra, jaridar Die Tageszeitung ta yi tsokaci ne game da sako jagoran kungiyar Biafra Nnamdi Kanu daga gidan yari makonni hudu da suka wuce. Shekaru 50 kenan cif da yunkurin al'ummar Igbo na ballewa daga Najeriya don kafa kasar Biafra. Yunkurin da ya haddasa yakin basasar kasar da ya yi sanadiyar mutuwar mutane miliyan biyu da rabi.

Shi dai Kanu ya yi da'awar cewa rashin adalci tsakanin Arewa da kuma Kudu ya sanya farfado da akidar Biafra. Ya na mai cewa ana nunawa 'yan kabilar Igbo wariya inda aka mayar da su ba a bakin komai ba.

Ita kuwa jaridar Der Tagesspiegel ta maida hankali ne kan yaki da cutar zazzabin cizon sauro a Tanzaniya.Jaridar ta yi nuni da yunkurin Fred Okumu wani likita matashi dan kasar ta Tanzaniya wanda ya dukufa da nazarin bincike kan yaki da Maleriya ta hanyar amfani da gidan sauro.

Okumu ya ce ko da yake amfani da maganin feshi wajen kashe sauro ya taimaka wajen rage yaduwarsa, akwai bukatar dakile yaduwar sauro tun daga tushe ta hanyar kashe kwaikwayensa kafin ya kyankyanshe.

Hukumar Lafiya ta Duniya dai ta yi kiyasin cewa a shekarar da ta gabata an sami karuwar mutane miliyan 214 da suka kamu da cutar a Afirka inda a duk mintina biyu yaro daya ke mutuwa saboda cutar cizon sauro ta Maleriya.