Badakalar cinikin jarirai a Nijar | Labarai | DW | 23.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Badakalar cinikin jarirai a Nijar

Ma'aikatar shari'a ta Jamhuriyar Nijar ta cafke ministan kula da harkokin noma na kasar Malam Abdou Labo tare da iza keyarsa zuwa gidan kaso.

Rahotanni dai sun nunar da cewa an iza keyar Malam Abdou Labo zuwa gidan kaso na garin Say da ke da nisan kilomita 60 da ga Yamai babban birnin kasar. A safiyar wannan Asabar ne dai babban alkalin Jamhuriyar ta Nijar ya gayyaci ministan zuwa kotu inda bayan ya saurare shi ya dauki matakin tsare shi. Kawo yanzu dai babu wani bayani da hukumomin shari'ar su ka yi dangane da dalillan tsare ministan, sai dai wakilinmu na Yamai Gazali Abdou Tasawa ya ruwaito cewa wasu na ganin matakin ba zai rasa nasaba da zargin da ake yi masa na hannun cikin badakalar cinikin jarirrai da ake zargin wasu 'yan Nijar sun yo daga makwabciyarta Tarayyar Najeriya. Yanzu haka dai sama da mutane 20 da ake zargi da hannun a cikin wannan badakalar na tsare a gidajen kurkuku daban-daban na kasar daga ciki har da matar ministan kula da harkokin noman Abdou Labo da kuma matar shugaban majalisar dokokin kasar Malam Hama Amadu.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa.
Edita: Pinado Abdu Waba/ LMJ