Badakalar cin hanci a wasannin Tennis a duniya | Labarai | DW | 18.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Badakalar cin hanci a wasannin Tennis a duniya

A cewar bayanan da aka bankado masu shirya wasannin na Tenis nada masaniya cewa 16 daga cikin manyan 'yan wasan Tenis 50 a duniya an samu hannunsu a harkokin karbar cin hanci.

Tennis - ATP Novak Djokovic

Novak Djokovic

Wasu bayanai na sirri da kafar yada labarai ta Buzzfeed da ma gidan rediyon BBC suka samu sun nunar da cewa an yi zamba cikin aminci a wasu manyan wasannin Tennis da aka tsara ciki kuwa har da gasar Wimbledon.

A cewar bayanan masu shirya wasannin na Tenis nad a masaniya cewa 16 daga cikin manyan 'yan wasan Tenis 50 a duniya an samu hannunsu a harkokin karbar cin hanci kafin buga wasa amma hukumar wasannin ba ta yi komai a kai ba.

Bayanan har ila yau sun nunar da cewa a akwai 'yan caca a Rasha da Italiya da suka tuntubi wasu 'yan wasa a wasu otel-otel da ma basu kudi tsaba dala dubu 50 ko ma sama da haka.

Sai dai a cewar kungiyar kwararrun masu wasannin na Tenis basu boye komai da ake zargi, kamar yadda Chris Kermode shugabata ke cewa:

"Sashin kare martabar wasannin na Tenis da ma hukumar tsara wasannin sun yi watsi da duk wani zargi na cewa suna boye wasu bayanai na ayyukan cin hanci ko kuma basa gudanar da bincike, sannan bayanan na BBC da Buzzfeed na bayani ne kan wasu abubuwa da suka faru shekaru goma da suka gabata. Duk wani abu sabo zamu bincike shi kamar yadda muka saba."