Badakalar cin hanci a kasar Ghana | Siyasa | DW | 03.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Badakalar cin hanci a kasar Ghana

Wata babbar badakala ta kuno kai a cibiyar ma’aikatan kula da tsarin aikawa da daliban da suka kamala karatun jami’a zuwa aikin bautatar kasa.

A daidai lokacin da gwamnatin kasar Ghana ke kokarin neman mafita dangane da sharadin da Asusun ba da Lamuni na Duniya na IMF ya gindaya mata, na cewa ta dakatar da yin karin albashi ga ma'aikatanta gabanin samun gudummuwa don farfado da tattalin arzikin wannan kasa, sai kawai aka samu badakalar da ta kuno kai na yin sama da fadi da milliyoyin Ghana Cedi, da wasu manyan Daractocin cibiyar kula da tsarin bautatawa kasa suka yi .

A bayyanin da tayi, hukumar kula da bincike ta kasar ta ce wannan al'amari kawai cin hanci ne da karbar rashawa da aka samu tare da hadin bakunan daractocin, tun daga abin da ya kama na yankunan karkara har zuwa birane. inda wasu daractoci a birnin Accra suka shirya sunanaki mutane na jabu a matsayin dalibai da a karshen ko wane wata gwamnati zata rinka biyan su amma kuma ba tare da an gan su a zahiri ba. Yanzu abin jira a gani shi ne ko wadanne matakai ne Hukumomin kasar ta Ghana zasu dauka kan masu hannu cikin wannan lamari dake mayar da hannun agogo baya ga kokarin da kasar keyi na neman bunkasa.