1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Badakala a batun gina layin dogo

Ubale Musa/USUAugust 11, 2015

Ana zargin dalar Amirka miliyan dubu daya da aka ranto domin kyautata aikin jiragen kasa a Najeriya gwamnatin PDP ba ta yi aikin ba.

https://p.dw.com/p/1GDbc
Eisenbahn Nigeria
Hoto: DW/M.Bello

A batun cin hanci da rubda ciki wanda aka bankado na baya-baya dai na zaman yanda aka karkatar da kudin Layin dogo wanda gwamnatin ta shude ke yin alfahari da yi. Tun kafin nan dai dama mahukuntan na Abuja sun dauki lokaci suna karajin yanda aka yi wakaci ka tashi da dubban miliyoyi na daloli a cikin kiftawar ido ba Bismilla. To sai dai kuma daga dukkan alamu yakin na neman hada yaki na siyasar da ya kalli yayan jam'iyar PDP ta adawa kallon turjiya da kukan da biyu.

Kama daga shi kansa tsohon shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan da ya kai har ga zuwa tattaki fadar gwamnatin kasar da nufi na korafi kan yakin ya zuwa yan majalisun dattawan jam'iyyar ta PDP da suka fitar da sanarwa ta hadin gwiwa dai, damuwa ya zuwa yanzu na zaman salon da yakin ke tafiya a kai, da kuma ya koma ambato a kafafe na jaridu sannan kuma da tozartarwa ta jami'an tsaro.

Abun kuma da ya kai kwamitin sulhunta tsakani na bangarori na siyasar ganawa da tsohon shugaban da magajinsa da ke fadar yanzu dama ragowar manyan shugabanni na siyasa da nufin neman hanyar kaucewar rikici. Karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Janar Abdusalamu Abubakar mai ritaya dai, 'yan kwamitin sun share lokaci suna ganawa da Buharin da nufin ji daga bakinsa bisa salo na yakin da ya tada hankali na masu halin berar cikin kasar a halin yanzu.

Comrade Tanko Yunusa dai na zaman shugaban jam'iyyar NCP kuma daya a cikin 'yan kwamitin da suka gana da Jonathan da ke Abuja, tun daga makon jiya kan batun. Ga kuma abun da yake fadi game da tunanin na Jonathan bisa salon da yakin ke tafiya kansa. Inda ya yace a ganin tsohon shugaba Jonathan tamkar an mai da gwamnatinsa a matsayin jagora a fannin cin hanci.

Maida gwamnatin Jonathan jagora ga batun cin hanci, ko kuma kokarin yakar rashawa kan tsari dai, ya zuwa yanzu halin berar da ya baiyana a bainar jama'ar ya dora tsohuwar gwamnatin bisa matsayin da babu irinsa a tarihin kasar ta Najeriya na shekaru 50 da doriya.

To sai dai kuma daga dukkan alamu 'yan kwamitin sun kamalla ganawar tasu ba tare da sauyi ga tunanin mahukuntan na Abuja, bisa dabarun da suke bi waje ambato da muzantawa ga barayin dukiyar kasar ta Najeriyar karkashin mulkin malafar.

Bishop Mathew Hassan Kukah dai na zaman kakakin kwamitin da ya share lokaci yana kai gwauro da mari a Abujar, ga kuma abun da yake fadi bayan ganawar da Buhari. Inda Bishop din kansa yace kowa ma na goyon bayan Buhari a yaki da cin hanci, kai yace ko barawonma kansa yaka mata ya kunya abinda ke faruwa kasar bisa satar da ake yi wa dukiyar gwamnati.

Tuni dai Abujar ta kai ga kafa kwamiti na kwararru da nufin nazari ga dabarun yakin da nufin tabbatar da samun nasarar dake da muhimmanci ga al'ummar kasar da suka kalli samu da rashi na arziki sakamakon annobar hancin.

DW_Nigeria_Integration12
Bishop Matthew Hassan KukahHoto: Katrin Gänsler
Nigeria Goodluck Jonathan Abdulsalami Abubakar Muhammadu Buhari
Hoto: DW/Ubale Musa