Babu wani ɗan Najeriya da ya rasu a hatsarin Saudiyya | Labarai | DW | 12.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babu wani ɗan Najeriya da ya rasu a hatsarin Saudiyya

Mutane guda uku kwai 'yan Najeriya suka samu rauni a hatsarin da ya auku a masallacin Makka.

Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya ta sanar cewar babu wani ɗan Najeriya ko ɗaya wanda ya rasa ransa a hatsarin da ya faru a ranar Jumma'a da ta gabata a ƙasa mai tsarki.


Alhaji Abdullahi Muktar shugaban hukumar ya ce waɗanda suka samu raunin ana yin jiyarsu kuma suna samun sauƙi. Mutane 107 suka mutu yayin da wasu 200 suka jikkata a cikin masallacin na Makkan a lokacin da wata ƙugiya ta faɗo sakamakon iska mai tsananin.