Babu tabbas game da makomar fasinjojin jirgin sama da ya bata a Indonesia | Labarai | DW | 01.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babu tabbas game da makomar fasinjojin jirgin sama da ya bata a Indonesia

Ana kara nuna fargaba game da makomar fasinjoji kimanin 100 dake cikin wani jirgin sama da ya bata a kasar Indonesia sakamakon rashin kyaun yanayi. Jirgin saman samfurin Boeing 737 na kamfanin Adam Air ya aike da sakon neman taimako kafin masu sarrafa zirga-zirgar jiragen sama su daina jin duriyarsa. Ministan sufuri na Indonesia Hatta Radjasa ya ce an tura ma´aikatan ceto zuwa yankin Mamuju dake cikin lardin Sulawesi ta Kudu mai tazarar kilomita 750 kudu maso yammacin wurin da jirgin saman ya dosa dake arewa maso gabashin tsibirin na Sulawesi.