Babu magani farar daya na yaki da corona | Labarai | DW | 03.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babu magani farar daya na yaki da corona

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa duk da kokarin da ake yi na gaggawar  samar da allurar rigakafin cutar corona, babu wata almara ko magani farar daya na yaki da cutar.

Kungiyar lafiyar ta duniya ta yi gargadin cewa duk da kokarin da kasashe da hukumomi na kasa kasa da kasa suke yi na gaggawar  samun allurar rigakafin cutar corona, babu wata almara ko magani farar daya na cutar.

Shugaban hukumar lafiyar ta duniya Adhanom Ghebreyesus da yake jawabi yayin wani taro ta bidiyo ya bukaci dukkan kasashen duniya su karfafa matakan kariyar lafiya kamar amfani da kyallen rufe baki da hanci da bada tazara a tsakanin juna da wanke hannu da kuma yin gwaji.

Shugaban hukumar ta WHO ya kara da cewa a halin da ake ciki an shiga mataki na uku na gwajin magani cutar kuma ana fatan samun alluran rigakafi na yaki da cutar.