Babu cigaban a zo a gani Masar tun hawan Mursi kan karagar mulki | Siyasa | DW | 04.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Babu cigaban a zo a gani Masar tun hawan Mursi kan karagar mulki

Murna ta koma ciki a Masar bayan kifar da mulkin tsofan shugaban ƙasa Hosni Mubarak

Egypt's President Mohamed Mursi looks at documents at the start of the third Arab Economic, Social and Development Summit, on January 21, 2013, in Riyadh. Saudi Arabia is hosting the two day summit aimed at relaunching regional cooperation in the face of economic challenges which were at the root of the Arab Spring uprisings. AFP PHOTO/FAYEZ NURELDINE (Photo credit should read FAYEZ NURELDINE/AFP/Getty Images)

Mohammed Mursi

Shekaru biyu bayan ƙaddamar da juyin juya halin da ya kifar da mulkin shugaba Hosni Mubarak na Masar, ƙasar ta tsinci kanta cikin wani hali na rashin tabbas dalili da tashe-tashen hankulan da ake fuskanta ba dare ba rana.

Bayan guguwar juyin juya hali ta biya da mulkin tsofan shugaban ƙasa Hosni Mubarak, al'umar Masar ta zaɓi Mohammad Mursi na jam'iyar 'yan uwa musulmi a matsayin saban shugaban ƙasa, wanda ta ɗorawa yaunin ƙaddamar da cenje-cenje, ta fannin haɓɓaka tattalin arziki, yaƙi da cin hanci da karɓar rashawa da kuma kyautata rayuwar jama'a.To saidai watani bakwai bayan hawan Mursi gadan mulki a yanzu al'umar Masar da dama sun fara cizon yatsa, tare da cewa ƙwanda bara da bana, inji kwaɗo da ya faɗa ruwan zafi.

Masu adawa da shugaban na zarginsa da rashin kataɓur tun daga lokacin da ya hau mulki har yanzu, hasali ma saban kundin tsarin mulkin da aka ƙaddamar, wanda kuma ya fara aiki ranar 26 ga watan Desemba na shekara da ta gabata,na fuskantar adawa mai tsanani, daga wani ɓangare na al'umar ƙasar.

A jimilice dai Mohammad Mursi yayi faɗuwar toto ruwa inji Hoda Salah, wata masanniyar kimiyar tattalin arziki:

Tace: Mutane da dama sun yi tsammani, idan 'yan uwa musulmi su ka hau karagar mulki za su taka mahimmiyar rawa wajen gudanar da adalci da tausayin jama'a, to amma yaban ya kasance tamkar yaban ɗan tukuru,domin a halin da ake ciki yanzu al'amura sai ƙara taɓarɓarewa su ke, tattalin arziki na kara durƙushewa sannan talauci na kara mayae jama'a.

Halin ƙunci da tattalin arzikin ƙasar Masar ya shiga ya samu asuli daga ƙauracewa yawan buɗe ido zuwa ƙasar, wanda a baya ke samar mata da kuɗaɗen shiga masu yawa.Bugu da ƙari kamfanonin su na dari ɗari da zuba jari kasancewar rashin tabbas da ƙasar ta shiga.

Bangaren 'yancin faɗin albarkacin bakin 'yan jarida na daga sassan da ba a cimma wata nasara a zo a gani ba, inda aka kwatanta da mulkin Hosni Mubarak inji Christoph Dreyer na ƙungiyar kare 'yancin aiki jarida ta ƙasa da ƙasa wato Reporters sans frontieres ko kuma Rerporters without borders::

"Har yanzu dai a na nan gidan jiya noman goje, ta fannin 'yancin albarkacin faɗin baki 'yan jarida.Idan ma an samu cigaba to irin na mai ginan rijiya ne.A shekara 2010, zamanin mulkin Mubarak,Masar na sahu na 127 ta fannin kiyaye haƙƙin 'yan jarida, amma a shekara 2012, ta cilla zuwa sahu na 158 daga jimlar ƙasashe 179 da ƙungiyar Reporters without borders ta gudanar da bincike.Wannan koma baya ya na da nasaba da zanga-zangar da ake shiryawa, inda kuma ake yawan tsangwamar kafofin sadarwa da ke tsage gaskiyar al'amuran da ke faruwa."

A yanzu babban ƙalubalen da shugaba Mohammad Mursi ke fama da shi ,shi ne laluben hanyoyin warware rikicin siyasar da ya rincaɓe a ƙasar inda 'yan adawa da baraden juyin juya hali suka baiyana buƙatar sai ya sauka daga karagar mulki, abinda magoya bayan 'yan uwa musulmi su ka ce ba za ta saɓu ba.

Banda rikicin siyasa na cikin gida shugaban ƙasar Masar na da baan aiki gabansa game da faɗakar da gamayyar ƙasa da ƙasa alkiblar gwamnatinsa da ake zargi da kasancewa mai tsatsauran ra'ayin kishin Islama.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin