Babu ci gaba a tattaunawar rikicin Gaza | Labarai | DW | 19.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babu ci gaba a tattaunawar rikicin Gaza

Har yanzu ba a kai ga samun matsaya ba kan rikicin Isra'ila da Falasɗinawa duk da kwanaki da aka yi ana tattaunawa.

Masu shiga tsakani na ɓangaren Isra'ila da Falsɗinawa sun tsawaita wa'adin tsagaita wuta, inda suke ci gaba da tattauna kawo ƙarshen farmakin da ake kai wa Gaza. Sa'o' ƙalilan kafin ƙare wa'adin a tsakan daren jiya Litinin suka ƙara tsawaita wa'adin da kwana guda.

Yazuwa yanzu faɗan ya yi sanadiyyar hallaka Falasɗinawa sama da 2000, galibi farar hula, yayin da aka kashe Yahudawa 67 galibi. A halin da ake ciki jagoran Falasɗinawa a tattaunawar Azzam al-Ahmad ya ce babu wani ci gaba ko ɗaya da aka samu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Abdourahamane Hassane