Babu adawa mai kwari a zaben Sudan | Siyasa | DW | 13.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Babu adawa mai kwari a zaben Sudan

Ana sa ran shugaban kasar mai ci Omar EL-Bashir zai yi tazarce domin akasarin jamiyyun adawar kasar suka kauracewa zaben.

Wannan dai shine karo na biyu tun daga shekarar 1986 da kasar ta Sudan ke shirya zabe a karkashin tsarin jam'iyyu barkatai. A karo na farko a shakara ta 2010 akasarin jamiyyun adawa sun bijirewa shiga zaben wanda ya baiwa shugaba Omar El-Bashir damar sake darewa kan karagar milkin kasar.

Sai dai masu lura da al'amurran siyasar kasar ta Sudan na ganin ko bana ma yar bara za a yi inda ake kyautata zaton zaben zai kasance irin na farautar bushiya ga shugaba El Bashir wato daga zungura sai dauka, domin akasarin jam'iyyun adawar kasar ba su shiga zaben ba ko a wannan karo.

'Yan adawa a kasar

Ko da ya ke duk da haka akwai 'yan takara 15 wadanda akasarinsu ba sanannu ba ne da za su fafata da shugaban mai ci, kuma mai jiran gado Omar El -Bashir dan shekaru 71 a yau a duniya. Sai dai wasu masu lura da tafiyar al'amurran siyasar kasar ta Sudan na ganin a wanann karo kan 'yan adawar ya fi kasancewa a hade. musamman idan aka yi la'akari da yarjejeniyar da su ka cimma a tsakanisu kafin zuwa zaben. Christian Delmet na wata cibiyar nazarin siyasar duniya ta Afrika na daga cikin masu irin wanann raayi.

Za a iya la,akari da wanann kira da baki guda da wasu kungiyoyin yan tawaye da kuma wasu jamiyyun adawar kasar su ka yi daga garin Adis Ababa inda su ka bukaci a kafa gwamnatin wucan gadi da zai sake tsara kasar akan hanyoyin democradiyya.kuma dukkaninsu sun amince da kawar da gwamnatin mai ci ta ko wani hali.

Rawar masu fafutukar kare hakkin dan adam

Biyo bayan wanann yarjejeniya ce ma dai gwamnatin kasar ta Sudan ta kama wasu masu fafutkar kare hakkin biladama da kuma ke adawa da milkin shugaba El-Bashir su biyu kafin daga bisani ta sake su. A cikin wanann yanayi na yi ma yan adawar barazana ne dai kasar ta Susan ke shirya wanann zabe wanda Christian Delmet na cibiyar nazarin siyasar duniya ta Afrika ya ce ba za su wani tasiri ba a idon kasashen duniya.

A siyasance wadannan zabuka ba su da wata ma,ana domin dan takara daya ne kawai za a ce ke da akwai da zai papata da mutanan da ba su da kowa a tare da su .dan haka wadanann zabuka su da banza duk daya.

Mutane miliyon 13 ne dai su ka cancanci kada kuri,ar daga cikin mutun milyon 38 na kasar ta Sudan.