Babban zabe a Mozambik | Labarai | DW | 15.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babban zabe a Mozambik

Masu kada kuri'a a babban zaben kasar Mozambik sun yi dandazo zuwa rumfunan zabe, domin kada kuri'unsu a zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dattawa.

Wannan dai na zuwa ne watanni kalilan bayan da bangarorin siyasar kasar biyu wato Frelimo da Renamo da ke gaba da juna na tsahon shekaru biyu suka cimma yarjejeniyar sulhu a tsakaninsu. Bayan da ya kada kuri'arsa a Maputo babban birnin kasar, shugaban jami'iyyar adawa ta Renamo Afonso Dhlakama ya bayyana cewa ya na da tabbacin zaben zai gudana cikin gaskiya da adalci . Shima dai Filipe Nyusi dantakarar jam'iyya mai mulki ta Frelimo ya kada kuria'ar ta sa ne a birnin na Moputu, yayin da dantakarar sabuwar jam'iyyar "Mozambique Democracy Movement" Daviz Simango ya kada kuri'arsa a birnin Beira da ke zaman birni na biyu mafi girma a kasar ta Mozambik.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu