Babban taron jam′iyar LND ta Bama | Labarai | DW | 10.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babban taron jam'iyar LND ta Bama

Magoya bayan jam'iyar LND sun jaddada goyan baya ga Aung San Suu Kyi a matsayin shugaba.

A kalla wakillai daga sassa daban daban na kasar Bama 850 ne suka halarci taron Congres na jam'iyar LND ta 'yar adawar nan bugu da kari mai lambar Nobel Aung San Suu kyi,suka sake jaddada mata goyon bayansu inda aka sake nada ta jagorar wannan jam'iyar.

Tun a ran juma'ar da ta gabata ne aka bude zaman taron jam'iyar a birnin Rangoun na kasar ta Bama,inda mahalarta taron suka duba ci-gaba da koma bayan da jam'iyar ke fiskanta a daidai lokacin da ake shirye shirye shiga zabe nan da shekaru biyu masu zuwa.

Jam'iyar dai ta share sama da shekaru 20 a cikin buya a dangane da barazanar da magoya bayanta ke fuskanta daga hukumar koli ta sojojin dake jagorancin kasar.

A shekarar bara ne dai aka zabi Suu kyi a matsayin 'yar majalisar dokokin kasar ta Bama bayan da jam'iyar ta ta lashe zaben da gagarumin rinjaye. To saidai kamar kowace jam'iya,ita ma LND na fuskantar 'yan matsaloli da suka hada da na jagoranci inda wasu ke kalubalantar Miss Suu kyi da yunkurin mallake komai daga jam'iyar.

Mawallafi: Issoufou Mamane.
Edita: Yahouza Sadissou Madobi