Babban taron ƙasa na jam′iyar ANC | Labarai | DW | 17.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Babban taron ƙasa na jam'iyar ANC

Jacob Zuma ya yi alƙawarin yaƙi da rashin ɗa'a a jam'iyarsa ta ANC

Jam'iyar ANC dake riƙ da ragmar mulki a frika ta Kudu ,a cigaba babban tarota na ƙasa.

A jawabin da ya gabatar gaban mahalarta taron, shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya yi alƙawarin ƙara matsa ƙaimi wajen yaƙi da zaman kashe wando, da yayi wa matasa kanta, a wannan ƙasa, sannan ya yi kira ga masu zuba jari daga ƙasashen duniya su ƙara ba da amana ga hada-hada tare da kamfanonin ƙasar.Zuma ya ƙuduri aniyar yaƙar wasu mummunan ɗabi'o'i a cikin jam'iyar ANC:

Yace:mun yi Allah wadai da tashin-tashina da kashe-kashen dake wakana na shugabanin jam'iya, sannan mun yi Allah wadai ga duk wasu aiyuka masu nasaba da cin hanci da rashawa, ba za mu yaƙi da rashin ɗa'a a cikin jam'iya.

A ƙarshen taron jam'iyar za ta zaɓi sabin magabata.

Jacob Zuma na fuskantar ƙalubale daga mataimakin shugaban jam'iyar Kagalema Motlanthy.Saidai ƙiddidigar jin ra'ayin jama'a ta tabbatar da cewa ,idan ba wata ƙaddara ba daga indallahi, Zuma zai samu gagaramar nasara.

Wannan taro na wakana a daidai lokacin da al'umar ke zargin hukumomin ƙasar da almubazaranci da kuma cin hanci da rashawa.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman